Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a yau Talata ya bayar da umarnin rushe gidajen karuwai da sauran guraren aikata baɗala a Maiduguri, babban birnin jihar. Zulum ya ba da umarnin ne a wata ziyara da ya kai unguwar ‘Bayan Quarters’, wani matsugunin da ke kusa da ma’aikatan layin dogo da ake kyautata zaton na dauke da masu aikata laifuka, karuwai da masu safarar miyagun kwayoyi. Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yawaitar ayyukan laifi da ke da alaka da gidajen karuwai, ya kuma umurci hukumomin gwamnati da su tarwatsa su cikin sa’o’i 72. Ya yi nuni da cewa, ayyukan na kawo barazana ga tsaro domin ƴan iska na ci gaba da dagula al’amuran zamantakewa da ke kawo cikas ga rayuwar al’umma da mutuncin daidaikun mutane. Mista Zulum ya bayyana cewa, yayin da za a rushe gidajen da ke tattara masu aikata laifuka da yin lalata da kananan yara mata a cikin sa’o’i 72, su kuma gidajen karuwai an bada sa’o’i 12 su rufe gidajen.