Ko Jonathan Be Isa Ya Gina Coci A Jamai'ar Bayero ba- Inji marigayi.
Zaman babbar kotun Shari'ah (Federal High Court) dake babban birnin tarayya Abuja, akan karar da kungiyar Kiristoci ta kasa CAN ta kai Masarautar Kano, saboda Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dr
Ado Bayero yasa an rushe wata Coci da ake ginawa a cikin tsohuwar Jami'ar Bayero Kano (BUK).
A zaman kotun da akayi a ranar Litinin 3 Feb, 2014, kotu ta nemi Mataimakin Shugaban Jami'ar Bayero Prof Rasheed, da wakilin kungiyar Kiristoci ta kasa, da kuma Mai Martaba Sarkin Kano da su bayyana a gabanta, a zaman kotun, anga Prof Rasheed da mataimakin shugaban CAN sun mike tare da Lauyoyinsu amma ba a ga Mai Martaba Sarki ba.
Daga nan sai Alkalin yace tunda muna da sauran mintuna 10 kafin fara Shari'ar zamu jira zuwan Mai Martaba Sarkin kano kafin wadannan mintoci su Cika.
Daga nan sai Justice ya dubi Prof
Rasheed yace a baya Kotu ta baku
umarnin Gina Coci a Jami'ar Bayero, ko kunbi umarnin kotu?
Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa munbi umarnin Kotu, dan sai da ginin Cocin ya kai linta sannan Mai Martaba Sarkin Kano ya bamu umarnin tsayar da aikin, daga baya kuma sai ga Mai Girma Galadiman Kano Alh. Tijjani Hashim ya jagoranci
Rushe ginin gaba daya. Justice yace, kuna nufin kenan kunyi watsi da umarnin kotu kunbi na Sarki? Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa saboda Sarki Ubanmu ne, kuma shine Sarki mai daraja ta daya a kasar nan bayan Sarkin
Musulmi saboda haka, bazamu iya kin yi masa biyayya ba.
Daga nan sai Justice ya umarci Prof
Rasheed da ya zauna. Justice ya ce da wakilin CAN kaji abinda ya fada kana da abin cewa?
Sai yace Eh, wakilin CAN yace gaskiya ne hukumar Makarantar Jami'ar Bayero ta fara gina Cocin aka Hanasu saboda haka muke rokon wannan kotu da ta hukunta Sarkin Kano bisa shiga hurumin da ba nasa ba. Daga nan shima akace ya zauna.
Sannan kotu ta nemi Sarkin daya
bayyana a gabanta, ana haka sai ga
Sakataren Gwamnatin Tarayya
Dr. Anyi Pius Anyim ya bayyana a gaban kotun, anga Alkalan kotun sun mike tsaye domin girmamawa gare shi,
Daga nan Dr. Anyim yace ya Mai Shari'ah ni ne wakilin Mai Martaba Sarkin Kano, ya umarceni dana
wakilceshi a wannan kotu domin amsa kira. Justice yace, kana nufin kana tsaye anan a matsayin Maimartaba Sarki kenan?
Dr. Anyim yace kwarai kuwa, kuma duk abinda zan fada ba ni na fada ba His Royal Highness ne ya fada. Justice yace, muna jinka.
Dr. Anyim yace, Sarki yace na sanar da wannan Kotu shi yasa a rushe Cocin, badan komai ba sai dan basa bukatar ganin cocin a Jami'ar, Sannan yace na gayawa wannan kotu mai daraja cewar, idan za'a gina Coci sau 10 a Jami'ar to
kuwa zai sa a rusheta sau 10
Sannan Galadiman Kano Alh. Tijjani Hasheem yace na gayawa wannan Kotu ko Shugaban kasa Goodluck Jonathan bai isa ya gina Coci ba a harabar Jami'ar Bayero, ba tare da yardar Mai Martaba
Sarki ba, Dr. Anyim ya cigaba da cewa, wannan shi ne sakon da Mai Martaba Sarkin Kano da Mai Girma Galadiman
Kano suka turo ni domin na sanarwa da wannan kotu nagode. Daga nan,sai
Alkalan Suka fara
tattaunawa a tsakaninsu, kafin daga bisani akaga Babbansu ya daga waya yana magana, daga nan sai Alkalin yace to duk munji baya nan ku, dan haka, wannan kotu tana kira ga Shugaban kasa daya duba wannan
Lamari idan yaga da
yiwuwar gina Cocin to ya bada umarnin ginin, idan kuma yaga ba sai an gina ba to shikenan.
Daga karshe Kotu ta Sallami wannan Kara, kuma tare da yiwa Mai Martaba Sarkin Kano fatan alkhairi da fatan Allah ya kara
masa lafiya da adalci.
Sai dai bayan gama wannan Shari'ah, Mai Girma Galadiman Kano, ya bayar da sanarwar cewa Babbar Mai Shari'ah ta kasa Justice Maryam Aloma Mukhtar da Alkalan kotun da suka jagoranci Shari'ar
da su gurfana a fadar Mai Martaba
Sarkin Kano, inda yace musu ya yadda ayi Coci a BUK Amma Sai dai in sun yadda duk Jami'oin Dake Kudu da arewacin Najeriya za a Gina Masallacin Jumaa a ciki. Ance tunda Suka tafi zancen Bai Kara tashi bah
Allah Ya Jaddada Rahama Ga Sarkin Kano.
Comments
Post a Comment