Kamar yadda car wash yake shima body wash haka yake to amma ana cire wasu chemical a canja su da wasu kamar yadda zaku gani anan gaba haka kuma ana iya saka masa kowacce irin kala misali
• Koriya
• Ja
• Yelluwa
• Shudiya
da dai sauran su
Haka kuma ana iya saka masa kowanne kalar qamshin turare misali
Lemon
Strawberry
Apple
Da dai sauran su.
Adadin Yawan Chemicals Da Yadda Ake Hadawa
Wannnan adadin idan aka gama shi zai baka daidai da yawan lita 20
1. CMC Natrosol 1/8 na kilo wato kaso daya cikin takwas za a jiqa shi da ruwa lita 10 a babbar robar da zata iya dauke duka Lita 20 idan an gama,
sai a juya sosai zai yi kauri kamar sitati.
2. Sodium lauryl sulfate 1/8 na kilo za a jiqa shi da ruwa Lita 1
3. Texapon 1/2 na kilo shi ba gari bane ruwa ne mai kauri ana zuba shi ne a cikin CMC a juya sosai
4. Gishirin girki 2/3 na kilo za a jiqa shi da ruwa lita 2 idan aka zo zuba gishiri a tace shi a watsar da wanda bai narke ba a yi amfani da ruwan sa.
5. Glycerine kamar ruwa yake ana zuba kaso daya cikin 4 na lita (1/4)
6. Vitamin E ana zuba 100ml yadda zaku gane wannan adadi shine ku duba sirinji Wanda ake yiwa mutane allura zaku ga 10ml ne.
7. Turare irin qamshin da kake so zaka zuba adadin 50ml ko 100ml
8. Kala ita ma gari ce zaka debi cikin qaramin cokali zaka jiqa ta da ruwa lita 1
Yadda Ake Hadawa
Za a fara zuba Texapon a cikin CMC a juya sosai sannan a riqa daukar sauran jiqaqqun chemical daya bayan daya ana zubawa a tabbatar duk wanda aka zuba sai an juya sosai sannan za a zuba na gaba.
Idan aka zuba komai sai a qara ruwa yadda ake son kaurin sa ya kasance ko kuma daidai da yadda zai bada adadin lita 20 gaba daya.
Idan aka kammala zuba komai sai a juya sosai sannan a barshi sai ya kwanta kamar bayan awa 10 zuwa 20 sannan a zuba a robobi a kai kasuwa.
Comments
Post a Comment