Barkanku da kasancewa da wannan shaf na mujallarhausa mai albarka, Ayau mun kawo muku hanyar da zaku hada sabulun wanki cikin sauki domin taimakama al’umma musamman matasan mu hausawa. su samu aikin yi Kuma har ila yau zamuyi bayani gamsashe akan inda zaka samu sinadaran da zaka hada sabulun ka cikin hanya mai sauki.
Tsokaci Game da Sabulun Wanki
Kamar yadda kowa dai ya sani ana amfani ne da shi wajen yin wanki, kuma shi na amfanin kullum ne lokacin sanyi ne koko a lokacin zafi duk ana amfani da sabulu don a wanke kaya domin ba mai bukatar kazanta.
Sinadaran da ake hadawa da su
Da farko yana da kyau mai son ya hada ya san sinadaran da ake hadawa subada sabulu, shiyasa zamu fara jera su sannan mu tafi akan yadda ake hada kayan su koma sabulun wanki lafiya lau.
Lissafin Sinadaran da Ake Bukata:
1. Costic soda
2. Soda ash
3. Sulphat
4. Silkate
5. Man kwakwa
6. Kala (ta ruwa gamasu bukata)
7. Kwankwani
8. Roba ko mazubi
9. Ma’auni (misali lidde)
10. Safar hannu
Matakan da ake bi wajenh Tsimin sinadaran su koma sabulun wanki
Tunda munga jerin sinaran da ake bukata wajen hada sabulu yazu kuma inshallahu zamu yi bayani akan matakan da ake bi wajen tsuma sinadaran.Dafarko dai zaka samu robobin ka guda uku lafiyayyu ba dole sai ruba ba mazubin ka guda uku, bayan ka samesu sai ka samo ruwa shima ka aje a kusa da kuma abunda za ka yi amfani da shi a matsayibn ma’auni kar ka canzashi har mu gama misali lidde ko wani kofi idan ka tanaji wadannan abubuwan da na ambata to sai mu je a cikin aiki;
A Kula a nan zan yi amfani da lidde a matsayin ma’auni na To ga matakan da yakamata mai karatu ka kiyaye kuma ka bi su sau da kafawajen hada sabulun ka,
1. Mataki na daya
Zuba lidde ko ma’auninka uku na ruwa a cikin roba ko mazubi na daban, sai ka deba costic soda ludayi uku itama lidde uku ka zuba a cikin ruwan da ka zuba a robar.
2. Mataki na Biyu
Debo ruwa kashi daya bisa hudu(1/4) na ma’aunin da kai amfani da shi na costic soda ka zuba a cikin wata robar har ila yau itama soda ashe kadebo kashi daya bisa hudu ka zuba a cikin ruwan, itama sulphat kayi mata irin na soda ash. Bayan kayi haka sai ka zuba su a wurin da ka hada costic soda din ka.
3. Mataki na ukku
Ka dauko silket shima kashi daya bisa hudu(1/4) na ma’auninka ka sa a cikin ihadin gukan su. Daga nan kuma sai ka dauko man kwkwar ka ka sa ma’auni biyu a cikin kwabin da ka yi, ka zuba kala taruwa in kanason yayi kala da kuma turare ga me son kamshi, to sa ka cigaba da motsawa zakaga ruwan yana warewa daban sablun yana dunkulewa.
Da kaga ya dunkule wato sinadaran sun hade sosai sai ka samu gwangwaninka ka rinka zuba hadin ka ajiye shi har sai ya bushe to inshallahu zaka ga sabulunka ya hadu lafiya lau in kasa kala zaka ga yana kalar da kai in kuma ba kala zaka/zaki ganshi fari yayi tauri sai ka fitar dashi yadda kake so ka siyar.
Kuci gaba da kasancewa da wannan shafi domin cigaba da samun abubuwan da zaku karu dasu, domin neman Karin bayani kuyi mana Magana ta comment section.
Comments
Post a Comment