MASARAUTAR GUMEL TA SAKE FITAR DA SABBIN DOKOKIN SAUKAKA AURE Skip to main content

MASARAUTAR GUMEL TA SAKE FITAR DA SABBIN DOKOKIN SAUKAKA AURE

 


Masarautar Gumel da ke karamar a da ka’idoji da za a bi don ganin hidimar aure ya saukaka a yankin.

Sanarwar na ƙunshe ne cikin wata takarda da ta fito daga Masarautar ta Gumel mai ɗauke da sanya hannun sakataren masarautar Alhaji Murtala Aliyu .

Inda takardar ta bayyana wasu dokoki guda goma sha tara da masarautar ta gindaya kan aure, tun daga kan akwati zuwa bikin aure da kuma daukar amarya.

Dokokin Su Ne kamar Haka:


1. Ba a ƙayyade sadaki ba amma kar yafi karfin aljihu duba da yadda tattalin arziki yake a kasar.

2. Kayan akwati kuwa kar su wuce Tufafi Shida (6) .

3. Takalma kar su fi kafa uku (3).

4. Ɗan kunne da sarƙa uku (3).

5. Mayafi da hijabi suma uku (3).

6. Ɗankwali uku (3).

7. Kayan kwalliya kar su fi saiti biyu (2).

8.A jimmila dai ba a son kudin hada lefe ya wuce Naira Dubu Dari (100,000).

9.An soke mata su kai lefe sai Maza ne zasu riƙa kaiwa.

10. An hana biyan kuɗin na-gani-ina-so

11. Kudin sa rana ma an hana.

12. An hana yin gara.

13. An hana yin kaɗe-ƙaɗe da raye-raye domin hakan na jawo chakuduwar maza da mata.

14. Kada shagalin biki ya wuce daga karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma.

15. Motoci uku (3)kawai aka yarda su kai amarya.

16. Kai amarya kada ya wuce karfe 6:00 na yamma.

17. An hana duk wani bidirin biki irin su ƙauyawa day, Arabian night, Yoruba night da sauran su.

18. An hana hawan angwanci sai an nemi izinin fadar masarautar Gumel.


                  #AURE .                    #GUMEL

Comments

Popular posts from this blog

Mujallar Hausa: Yadda ake hada Sabulun wanki a Saukake

    Barkanku da kasancewa da wannan shaf na mujallarhausa mai albarka, Ayau mun kawo muku hanyar da zaku hada sabulun wanki cikin sauki domin taimakama al’umma musamman matasan mu hausawa. su  samu aikin yi Kuma har ila yau zamuyi bayani gamsashe akan inda zaka samu sinadaran da zaka hada  sabulun ka cikin hanya mai sauki. Tsokaci  Game da Sabulun Wanki Kamar yadda kowa dai ya sani ana amfani ne da shi wajen yin wanki, kuma shi na amfanin kullum ne lokacin sanyi ne koko a lokacin zafi duk ana amfani da sabulu don a wanke kaya domin ba mai bukatar kazanta.  Sinadaran da ake hadawa da...

Yadda Ake Hada Body Wash Ko Kuma Face Wash

Kamar yadda car wash yake shima body wash haka yake to amma ana cire  wasu chemical a canja su da wasu kamar yadda zaku gani anan gaba haka kuma ana iya saka masa kowacce irin kala misali • Koriya • Ja • Yelluwa • Shudiya  da dai sauran su Haka kuma ana iya saka masa kowanne kalar qamshin turare misali Lemon Strawberry Apple Da dai sauran su. Adadin Yawan Chemicals Da Yadda Ake Hadawa Wannnan adadin idan aka gama shi zai baka daidai da yawan lita 20 1. CMC Natrosol 1/8 na kilo wato kaso daya cikin takwas za a jiqa shi da ruwa lita 10 a babbar robar da zata iya dauke  duka  Lita 20 idan an gama, sai a juya sosai zai yi kauri kamar sitati.  2. Sodium lauryl sulfate 1/8 na kilo za a jiqa shi da ruwa Lita 1 3. Texapon 1/2 na kilo shi ba gari bane ruwa ne mai kauri ana zuba shi ne a cikin CMC a juya sosai 4. Gishirin girki 2/3 na kilo za a jiqa shi da ruwa lita  2 idan aka zo zuba gishiri a tace shi a watsar da wanda bai narke ba a yi amfani da ruwan sa. 5. Glyc...