Ministan Kudin Najeriya Wale Edun, ya ce
gwamnatin kasar ta fara tattaunawa da Bankin Duniya kan matakan da za a dauka wajen daidaita kasuwar hada-hadar canjin kudade a Najeriyar ta hanyar kawo karshen faduwar darajar naira.
A lokacin da yake yi wa manema labarai karin bayani a kan kokarin da suke yi, Ministan Kudin ya ce suna neman bankin duniyar ya ba su bashin ne daga asusunsa na tallafa wa kasashe masu tasowa da ke bayar da rancen kudade marasa kudin ruwa.
To sai dai, kwararre a fannin tattalin arziki Dr. Isa Abdullahi na Jami’ar Kashere, ya ce zabin karbo bashi don daidaita kasuwar canjin Najeriya ba zai warware matsalar rashin tabbas kan makomar Naira ba.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken bayaninsa a rahoton Nura Ado Sulaiman
Dangane da rashin kudin ruwa kan rancen kudin da gwamnatin Najeriyar ke nema daga Bankin Duniyar kuwa, Dr. Abdullahi ya ce ko shakka babu rangwame mai amfani aka sami amma fa nan ma da sauran rina a kaba.
A cikin makon nan da ke shirin karewa, sai da darajar naira ta fadi zuwa 1002 kan dalar Amurka guda a kasuwar bayan fage, sakamakon karancin dalar da ake fuskanta.
Comments
Post a Comment