Mujallar Hausa Skip to main content

Posts

Showing posts from October, 2023

Zulum ya bada umarnin rushe gidajen karuwai cikin awanni 72 a Maiduguri

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a yau Talata ya bayar da umarnin rushe gidajen karuwai da sauran guraren aikata baɗala a Maiduguri, babban birnin jihar. Zulum ya ba da umarnin ne a wata ziyara da ya kai unguwar ‘Bayan Quarters’, wani matsugunin da ke kusa da ma’aikatan layin dogo da ake kyautata zaton na dauke da masu aikata laifuka, karuwai da masu safarar miyagun kwayoyi. Gwamnan ya nuna damuwarsa kan yawaitar ayyukan laifi da ke da alaka da gidajen karuwai, ya kuma umurci hukumomin gwamnati da su tarwatsa su cikin sa’o’i 72. Ya yi nuni da cewa, ayyukan na kawo barazana ga tsaro domin ƴan iska na ci gaba da dagula al’amuran zamantakewa da ke kawo cikas ga rayuwar al’umma da mutuncin daidaikun mutane. Mista Zulum ya bayyana cewa, yayin da za a rushe gidajen da ke tattara masu aikata laifuka da yin lalata da kananan yara mata a cikin sa’o’i 72, su kuma gidajen karuwai an bada sa’o’i 12 su rufe gidajen.

Sanda Marigayi Ado Bayero ya Hana Gina Coci a B.U.K

  Ko Jonathan Be Isa Ya Gina Coci A Jamai'ar Bayero ba- Inji marigayi.  Zaman babbar kotun Shari'ah (Federal High Court) dake babban birnin tarayya Abuja, akan karar da kungiyar Kiristoci ta kasa CAN ta kai Masarautar Kano, saboda Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dr Ado Bayero yasa an rushe wata Coci da ake ginawa a cikin tsohuwar Jami'ar Bayero Kano (BUK). A zaman kotun da akayi a ranar Litinin 3 Feb, 2014, kotu ta nemi Mataimakin Shugaban Jami'ar Bayero Prof Rasheed, da wakilin kungiyar Kiristoci ta kasa, da kuma Mai Martaba Sarkin Kano da su bayyana a gabanta, a zaman kotun, anga Prof Rasheed da mataimakin shugaban CAN sun mike tare da Lauyoyinsu amma ba a ga Mai Martaba Sarki ba. Daga nan sai Alkalin yace tunda muna da sauran mintuna 10 kafin fara Shari'ar zamu jira zuwan Mai Martaba Sarkin kano kafin wadannan mintoci su Cika.  Daga nan sai Justice ya dubi Prof Rasheed yace a baya Kotu ta baku umarnin Gina Coci a Jami'ar Bayero, ko kunbi umarnin kotu? Prof Rashe...

Najeriya Za Ta Ciyo Bashi Don Farfado da darajar Naira

  Ministan Kudin Najeriya Wale Edun, ya ce  gwamnatin kasar ta fara tattaunawa da Bankin Duniya kan matakan da za a dauka wajen daidaita kasuwar hada-hadar canjin kudade a Najeriyar ta hanyar kawo karshen faduwar darajar naira.  A lokacin da yake yi wa manema labarai karin bayani a kan kokarin da suke yi, Ministan Kudin ya ce suna neman bankin duniyar ya ba su bashin ne daga asusunsa na tallafa wa kasashe masu tasowa da ke bayar da rancen kudade marasa kudin ruwa.  To sai dai, kwararre a fannin tattalin arziki Dr. Isa Abdullahi na Jami’ar Kashere, ya ce zabin karbo bashi don daidaita kasuwar canjin Najeriya ba zai warware matsalar rashin tabbas kan makomar Naira ba.  Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken bayaninsa a rahoton Nura Ado Sulaiman Dangane da rashin kudin ruwa kan rancen kudin da gwamnatin Najeriyar ke nema daga Bankin Duniyar kuwa, Dr. Abdullahi ya ce ko shakka babu rangwame mai amfani aka sami amma fa nan ma da sauran rina a kaba.  A...

MASARAUTAR GUMEL TA SAKE FITAR DA SABBIN DOKOKIN SAUKAKA AURE

  Masarautar Gumel da ke karamar a da ka’idoji da za a bi don ganin hidimar aure ya saukaka a yankin. Sanarwar na ƙunshe ne cikin wata takarda da ta fito daga Masarautar ta Gumel mai ɗauke da sanya hannun sakataren masarautar Alhaji Murtala Aliyu . Inda takardar ta bayyana wasu dokoki guda goma sha tara da masarautar ta gindaya kan aure, tun daga kan akwati zuwa bikin aure da kuma daukar amarya. Dokokin Su Ne kamar Haka: 1. Ba a ƙayyade sadaki ba amma kar yafi karfin aljihu duba da yadda tattalin arziki yake a kasar. 2. Kayan akwati kuwa kar su wuce Tufafi Shida (6) . 3. Takalma kar su fi kafa uku (3). 4. Ɗan kunne da sarƙa uku (3). 5. Mayafi da hijabi suma uku (3). 6. Ɗankwali uku (3). 7. Kayan kwalliya kar su fi saiti biyu (2). 8.A jimmila dai ba a son kudin hada lefe ya wuce Naira Dubu Dari (100,000). 9.An soke mata su kai lefe sai Maza ne zasu riƙa kaiwa. 10. An hana biyan kuɗin na-gani-ina-so 11. Kudin sa rana ma an hana. 12. An hana yin gara. 13. An hana yin kaɗe-ƙaɗe da raye...

Yadda Ake Hada Body Wash Ko Kuma Face Wash

Kamar yadda car wash yake shima body wash haka yake to amma ana cire  wasu chemical a canja su da wasu kamar yadda zaku gani anan gaba haka kuma ana iya saka masa kowacce irin kala misali • Koriya • Ja • Yelluwa • Shudiya  da dai sauran su Haka kuma ana iya saka masa kowanne kalar qamshin turare misali Lemon Strawberry Apple Da dai sauran su. Adadin Yawan Chemicals Da Yadda Ake Hadawa Wannnan adadin idan aka gama shi zai baka daidai da yawan lita 20 1. CMC Natrosol 1/8 na kilo wato kaso daya cikin takwas za a jiqa shi da ruwa lita 10 a babbar robar da zata iya dauke  duka  Lita 20 idan an gama, sai a juya sosai zai yi kauri kamar sitati.  2. Sodium lauryl sulfate 1/8 na kilo za a jiqa shi da ruwa Lita 1 3. Texapon 1/2 na kilo shi ba gari bane ruwa ne mai kauri ana zuba shi ne a cikin CMC a juya sosai 4. Gishirin girki 2/3 na kilo za a jiqa shi da ruwa lita  2 idan aka zo zuba gishiri a tace shi a watsar da wanda bai narke ba a yi amfani da ruwan sa. 5. Glyc...

Shin Ko Kasan A ina Kalmar vespa ta Samo Asali A kasar Hausa Kowa?

  Kalmar vespa ta Samo asali Daga wasp Wanda shine kwaron Da ya bayyana a hoton qasa kasancewa shi ainayin scooter yayi kama Da kwaron . A hausance Kuma Idan akace wasp ana nufin zanzaro Shima Bayan bahaushe ya Kalli kwaron Da Kuma yanayin tsukewar qugun qwaron!  A hausance zanzaro shine mutum yasaka qananun Kaya sai ya saka rigar acikin wandon! Zanzaro" A shekara ta 1946 aka Fara qirqirar Vespa A qasar Italy Wanda Kuma Kalmar vespa" Italian word ce ta samo asali Daga Sunan wasp Wanda wani qwarone bansan sunansa Da Hausa ba! Sbd kamancecinya Da vespa yake Da kwaron Sai ake Kiran scooter Da vespa!  Acikin dabi'a irin ta vespa shine is very friendly Yana Da matuqar shiga Rai Da Kuma dadin sarrafawa! Yana Da qarfi Da Kuma dadin yin parking Wanda zaka Iya parking Na vespa Kuma kayi kashingide akansa. Advantages  Na vespa Idan akayi Ruwan zaiyi wahala wani yabataka Ko Kuma kabata wani Da chabi, vespa akwai dadin Tuki musamman Da dare,  Vespa Yana Da lower centa of gr...